Jami'an hukumar NSCDC sun harbi wani 'dan banga a jihar Bayelsa

Jami'an hukumar NSCDC sun harbi wani 'dan banga a jihar Bayelsa

- Jami'an hukumar tsaro na NSCDC sun harbi wani dan banga yayin da ya yi yunkurin hana su tafiya da wata matar aure da suka zo neman mijin ta amma basu same shi ba

- Harbin da akayi wa dan bangar a hannu da kafa ya fusata matasan unguwar har ya kai ga sunyi zanga-zanga tare da rufe hanya

- Kwamandan hukumar NSCDC na jihar, Mista Godwin Nwachukwu ya tabbatar wa NAN faruwar lamarin amma ya ce ana gudanar da bincike domin sanin matakan da za'a dauka

Mun sama labarin cewa a safiyar yau Talata wasu jami'an tsaro na NSCDC sun harbi wani jami'in yan banga a Ikarama da ke karamar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa.

Kamfanin Dillanci Labarai NAN ya gano cewa jami'an na NSCDC sun tafi unguwar ne don kama wani mutum amma da basu same shi ba sai suka kama matar sa sanadiyar haka ne suka harbi dan bangar da ya yi yunkurin hana su tafiyar da matar.

Jami'in NSCDC ya harbe wani dan banga a jihar Bayelsa

Jami'in NSCDC ya harbe wani dan banga a jihar Bayelsa

KU KARANTA: Amurka da wasu kasashen za su rage sayan man fetur na Najeriya daga shekarar 2022

A cewar Mista Ben Warder, shugaban matasan yankin ya ce jami'an na NSCDC sun harbi dan bangar a hannu da kuma kafar sa, wannan lamarin ya fusata matasan unguwar har ta kai ga sunyi zanga-zanga inda suka rufe hanyar zuwa wata rijiyar man fetir na kamfanin shell inda akace jami'an na NSCDC sun tafi da matar.

Matar dan banagr da aka harba da korafin yadda lamarin ya jefa iyalan nasu cikin mawuyacin hali da kuma yadda mai gidanta ke fama da azaba sakamakon harbin da akai masa.

Shi kuma mutumin da aka zo kama wa, Mista Orukari Udoji ya ce yana cikin jeji inda ya ke sarar itace lokacin da jami'an na NSCDC suka tafi da matarsa sa, bayanai sun nuna cewa an zo kama shi bisa zubda gurbataccen man fetur a dajin da ya ke aiki, abinda da ya musanta aikatawa.

Kwamandan hukumar ta NSCDC na jihar Bayelsa, Mista Godwin Nwachukwu ya fadawa wa NAn cewa ya samu rahoton afkuwar lamarin, ya kuma aika jami'ai domin su gudanar ta bincike su sanar dashi asalin abin da ya wakana.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel