TSA: Duk wata Gwamnatin Buhari na adana kusan Naira Biliyan 25

TSA: Duk wata Gwamnatin Buhari na adana kusan Naira Biliyan 25

- Gwamnatin Shugaba Buhari ta adana Bilioyi ta tsarin asusun bai-daya

- Haka kuma an samawa matasa aiki ta irin su tsarin nan na N - Power

- An kuma kashe kudi wajen ayyukan titi da jirgin kasa a fadin Kasar

A duk wata Gwamnatin ShugabaBuhari na adana kusan Biliyan 25 ta asusun bai daya da aka dabbaka amfani da shi watau TSA a farkon hawan wannan Gwamnati. Kuma Buhari ya agazawa Jihohi 28 da su ka gaza biyan albashi da Biliyan 698.

TSA: Duk wata Gwamnatin Buhari na adana kusan Naira Biliyan 25
Shugaba Buhari yana adana Bilioyin kudi ta tsarin TSA

Mun ji cewa a kowane wata Najeriya na samun damar adana Biliyan 24.7 a Gwamnatin Buhari. Bayan nan kuma an adana sama da Naira Biliyan 108 wanda a da aka saba kashewa wajen biyan bankuna ladan ajiye kudin Gwamnati.

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi alhinin Marigayi Sheikh Tureta

Wani Farfesan tattali a Jami’ar Jihar Nasarawa wanda shi yayi jawabi a wani taro da kungiyar hadaka ta magoya bayan Shugaba Buhari ta hada ya kuma bayyana irin kokarin da wannan Gwamnati tayi bayan karyewar fetur a kasuwar Duniya.

Farfesa Uwaleke Uche yace bayan nan kuma Shugaba Buhari ya kahe fiye da Tiriliyan guda wajen ayyuka a fadin kasa. Tsarin TSA da kuma BVN da aka kawo ya kokarta wajen maganin barna a Najeriya kuma an samawa matasa ayyuka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng