Hukumar SUBEB ta hana wazifa a makarantun Tsangayar Bauchi
Rahotanni sun kawo cewa hukumar kula da ilimin bai daya wato SUBEB sashinj jihar Bauchi ta bukaci makarantun Tsangaya da su daina yin wazifa ko karanta salatul fatihi a hidimar makarantar.
A cewar hukumar hakan baya daga cikin tsarun makarantun a fadin jihar da ma tsarin hukumar UBEC ta fitar akan karatun Tsangaya.
Wannan bayani na tattare ne a wata takarda da shugaban hukumar ta SUBEB Yahaya Ibrahim Yaro ya fitar da sanya hannun sakataren hukumar Mahmeed A. Kari.
An saki wasikar ne a ranar 5 ga watan Fabairu mai taken wasikar dakatar da wazifa da salatil fatihi mai addireshi kai tsaye zuwa ga Shugabannin makarantun Tsangaya-Tsanya da suke fadin Bauchi.
KU KARANTA KUMA: An bankado mabuyar Femi Fani-Kayode bayan yayi wa Kotu karyar rashin lafiya
Hukumar ta yi bayanin cewar ta samu korafin cewar ana tilasta wa dalibai yin wazifa da salatil fatihi.
Jaridar Leadershin ta rahoto cewa wannan mataki bai yi wa mamallakin wannan makarantar Tsangayar Sheikh Dahiru Bauchi dadi ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng