An kama mutumin da ya ce kiran sallah na damunsa a Saudiyya

An kama mutumin da ya ce kiran sallah na damunsa a Saudiyya

- Wani marubuci mai suna Mohammed al-Suhaimi ya ce kiran sallah na damun sa

- Jami'an tsaron kasar Saudiya sun kama marbcin da yae kiran sallah na damun sa

Hukumonin tsaro na kasar Saudiyya sun kama wani marubuci mai suna, Mohammed al-Suhaimi, da yace masallatai sun yi yawa a kasar kuma kiran sallah na damunsa.

Hukumomi sun kama marbucin ne bayan sun kammala yi masa bincike.

Mohammed al-Suhaimi ya soki yadda ake gudanar da kiran sallah, yana mai cewa yawaita kiran salla da kuma yadda masallatai ke amfani da na’urar lasifika wurin kira sallah yana hana mutane bacci da kuma damun kananan yara.

An kama mutumin da ya ce kiran sallah na damunsa a Saudiyya
An kama mutumin da ya ce kiran sallah na damunsa a Saudiyya

Marubucin, wanda ya yi suna wajen sassaucin ra'ayi, ya yi tsokacin ne lokacin da yake hira da wani gidan talbijin na kasashen Larabawa.

KU KARANTA : Gwamnatin jihar Kaduna ta rusa ofishin sashen jam’iyyar APC da ta dakatar da El-Rufai

Tsokaci nasa ya janyo masa caccaka daga wurin masu amfani da shafukan sada zumunta a duniya.

A baya dai, hukumomin Saudiyya sun sanya wasu matakai da suka umarci a rika rage karar na’urar lasifika lokacin ake kiran sallah tunda masallatai suna da yawa a kasar..

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel