Abubakar Tureta ya kasance mutun mai nagarta – Shugaba Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ta’aziyya akan marigayi malamin musulunci, Abubakar Tureta, inda yabayyana shi a matsayin mutun mai tarin sani da kyawawan hallaya wanda yayi rayuwarsa wajen wanzar da zaman lafiya a tsakanin mutane mabiya addini daban-daban.
A wata sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin malamin, shugaban kasa Buhari yace marigayin yayi rayuwa mai cike da gaskiya, za a kuma dunga tunawa da gudunmawar da ya bayar a rayuwarsa.
Shugaban kasar wanda ya bayyana mutuwarsa a matsayin faduwar babban bango a dajin ilimi, wanda ya ba da gagarumin gudunmawa a addinin Musulunci. Ya bukaci sauran malaman Musulunci da suyi koyi da tawali’unsa.
Shugaban kasar yace babban abun da mabiya Tureta, masoyansa da dalibansa zasuyi masa a yanzu shine koyi da kyawawan dabi’arsa.
KU KARANTA KUMA: Dole a kawo karshen barna da ke cikin harkar man fetur a Najeriya inji Shugaba Buhari
Shugaba Buhari yayi addu’an Allah ya gafarta masa ya kuma saka masa da aljannah sannan ya ba iyalansa hakurin rashinsa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng