Rikicin makiyaya: Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Adamawa a gobe
- Shugaba Buhari zai ziyarci jihar Adamawa a gobe Talata
- Hakan ya biyo bayan alkawarin day a dauka na ziyarar jihohin da rikicin makiyaya ya yi tsauri
- Haka zalika Buhari zai bude taron yaki daa rashawa a jihar da kuma kaddamar da wasu ayyuka
Rahotanni dake zuwa mana sun tabbatar da cewa a gobe Talata, 20 ga watan Fabrairu ne ake sa ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Adamawa.
Hakan ya biyo bayan alkawarin da ya dauka na kai ziyara a jihohin da rikicin Fulani makiyaya da manoma ta yi kamari.
A yayin ziyarar, shugaban kasar zai bude taron yaki da rashawa na jihar tare da kaddamar da wasu ayyukan raya kasa da Gwamnan jihar ya aiwatar.
KU KARANTA KUMA: Anyi ruwan kankara a Benin
Tuni dai, rundunar 'yan sanda ta haramta bin wasu hanyoyi a cikin jihar don inganta Harkokin tsaro a yayin ziyarar Shugaban.
A baya Legit.ng ta kawo cewa an yi nasarar kasha wata shu’umar dabba mai kama da kerkeci da ta bulla a garin Beli dake karamar hukumar Rogo.
Jaridar rariya ta rawaito cewar dabbar na cin naman dabbobi, karnuka, hard a ma mutane.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng