An yi jana'izar Sheikh Abubakar Tureta a Kaduna
- An yi jana'izar Sheikh Abubakar Tureta a safiyar ranar Litinin a jihar Kaduna
- Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmaed El-Rufai, yana daga cikin mutanen da suka halarci jana’izar Sheikh Abubakar Tureta
A safiyar yau Tatala aka yi jana’izar shahararren malamin addinin musulunci dake jihar Kaduna Sheikh Abubakar Tureta.
Sheikh Abubakar Tureta ya ya rasu ne a ranar Lahadi a Asibitin Garkuwa da ke birnin jihar Kaduna.
Anyi janaizar shehin malamin ne a cikin gidan sa da ke Tudun Wada layin Kosai Kaduna.
Marigayi Sheikh Abubakar Tureta ya mutu yana da shekarU 74 a duniya ya bar mata uku da 'ya'ya 39 da kuma jikoki 85.
KU KARANTA : Makiyaya suna ci gaba da kai mana hari a jihar Benue - Gwamna Samuel Ortom
An haifi Sheikh Abubakar Tureta ranar 5 ga watan Janairu 1944, kuma dan asalin jihar Sokoto ne dake Arewa.
Malamin yana daga cikin jiga-jigan malamin kungiyar Izalatul Bidi'a Wa Ikamatus (JIBWIS) Sunnah kuma ya taba rike shugabancin majalisar malamai na tsohuwar jihar Sokoto.
Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmaed El-Rufai, yana daga cikin manyan da suka halarci jana’izar Sheikh Abubakar Tureta, Sheikh Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya jagorancin sallar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng