Lamido ya tarbi masu sauya sheka zuwa PDP 5000 a Jigawa, ya sha alwashin kayar da Buhari a 2019
- Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa da jam’iyyar PDP sun sha alwashin kayar da shugaba Buhari a 2019
- Ya ce kudirinsa kudirin Allah ne sannan kuma ya bukaci mutane da kadda sun yi kokarin tokare shi
- Lamido ya kuma ce an azabtar da shi tare da kai shi gidan yari saboda hasashensa na son ganin an yada damokradiyya a kasar
Alhaji Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa sannan kuma dan takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP yayinda yake tarban sama da mutane 5,000 da suka sauya sheka daga APC zuwa PDP ya sha alwashin kayar da shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben 2019 idan har jam'iyyarsa ta basa tikitin takarar shugabancin kasa.
A ranar 17 ga watan Fabrairu, tsohon gwamnan a wani gangamin siyasa yayinda yake kaddamar da ofishin neman zabensa a karamar hukumarsa ta Birnminkudu dake jihar.
Da yake bayyana kudirinsa a matsayin al'ajabi, Lamido ya kalubalanci duk wanda ke mulki daga shugaban kasa har zuwa kasa da kadda suyi yunkuri hana Allah ikonsa, jaridar Independent ta rahoto.
Tsohon gwamnan ya kuma kalubalanci Buhari da ya fassara wasu yan zantuka da yayi a harshen Fulatanci a taron.
KU KARANTA KUMA: Hadimin gwamnan jihar Katsina ya kashe yarsa da mota
Lamido ya kuma yi ikirarin cewa Buhari da APC sun fada ma yan Najeriya karairayi a zaben 2019.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa wani abun bakin ciki ya faru a ranar Juma’a a jihar Katsina lokacin da mai ba Gwamna Aminu Masari shawarar na musamman akan al’amuran addini, Abdullahi Darma, ya take yarsa, A isha da mota bisa tsautsayi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng