2019: Hotunan taron bude ofishin takarar Sule Lamido a mahaifar sa
Tsohon gwamnan jihar jigawa kuma mai neman jam'iyyar PDP ta tsayar da shi takarar shugancin kasa a zaben 2019, Alhaji Sule Lamido, ya bude ofishin yakin neman zabensa na farko a mahaifar sa, karamar hukumar Birnin Kudu, a jihar Jigawa.
Kwamitin yakin neman zaben Sule Lamido ya bayyana cewar zasu bude ofishin yakin neman zabe a matakin jiha nan bada dadewa ba kafin daga bisani su bude ofisoshin yakin neman zabe a jihohin Najeriya 36.
Dubban mutane daga kananan hukumomin Jigawa da jihohi masu makwabtaka da ita sun halarci bikin taron bude ofishin.
DUBA WANNAN: 2019: Shugabancin jam'iyyar PDP ya tattauna wasu muhimman batutuwa da IBB
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng