Bashir Dodo yayi binciken da zai taimaki marasa lafiyar idanu
- Bashir Dodo yayi wani nazari da zai agazawa masu cutar idanu
- Dr. Bashir Dodo Malami ne Matashi ‘Dan asalin Jihar Katsina ne
- Wannan bincike da aka yi ya ci lambar yabo a wata Jami’ar waje
Mun samu labari cewa wani hazikin Matashi da ya fito daga Jihar Katsina yayi suna a Duniya inda ya kammala karatun sa na Digiri na uku watau PhD a wata Jami’ar kasar waje kwanan nan.
Bashir Isa Dodo wanda Malami ne a Jami’ar Katsina a fannin ilmin komfuta ya kirkiro wata hanya da za a bi ta taimakawa masu fama da larurar rashin lafiyan ido a Duniya. A Jami’ar ta Birnin Brussels wannan ta sa Dodo ya karbi lambar yabo.
KU KARANTA: An nemi Maza su kara auren mata a Jihar Imo
Wannan bincike na Bashir Dodo ta sa ya karbi kyauta a kasar inda aka tashi taron BIOMAGING na masana a shekarar bana babu kamar sa. Binciken na sa zai taimaka wajen gyara sashen retina da ke cikin idanun ‘Dan adam nan gaba a Duniya.
Likitocin idanu a Duniya za su amfana da wannan gudumuwa da Dr. Bashir Dodo ya kawo. Bashir asalin ‘Dan Jihar Katsina ne kuma yayi Digiri da Digirgir a fannin Komfuta inda ya kamalla a 2012.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng