Kokarin da Buhari yayi akan Boko Haram shine yasa ni barin jam'iyyar PDP - Ahmad Gulak
- Kokarin da shugaba Buhari yayi akan Boko Haram shine yasa ni barin jam'iyyar PDP
- A jiya ne Ahmed Gulak ya koma jam'iyyar APC tare da mutanen sa
- Ya koma tare da mutane kimanin 42,000
Tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara akan harkar siyasa, Ahmed Gulak, ya bayyana cewar, kokarin da gwamnatin shugaba Buhari ta yi akan 'yan kungiyar boko haram shine ya sashi canja sheka zuwa jam'iyyar APC din.
DUBA WANNAN: Siyasa: Ahmad Gulak ya koma jam'iyyar APC tare da mutanen sa
A jiya Asabar ne Ahmed Gulak ya tattara komatsansa tare da mutanen sa ya ce ya bar tsohuwar jam'iyyar sa ta PDP ya koma jam'iyya mai mulki wato jam'iyyar APC.
Tsohon mai bawa tsohon shugaban kasa shawarar ya ce ya bar jam'iyyar ta PDP ne, saboda an tilasta musu fita daga jam'iyyar, ta hanyar rashin adalci da kuma rashin hadin kai a cikin jam'iyyar.
A jiya ne muka kawo muku cewar Ahmed Gulak ya koma jam'iyyar APC tare da mutanen sa kimanin mutum 42,000. Inda ya har ya kara da cewar yanzu dai sun yi jana’izar PDP a Jihar Adamawa.
Sannan Ya ba da misalin yadda tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dinga canza jam’iyya har sau biyar, da nufin cewar kowa na da ‘yancin canza jam’iyya kamar yadda doka ta yardar wa duk dan kasa.
Atiku daga PDP, ya koma ACN, sannan ya dawo PDP daga nan ya koma APC gashi yanzu ya koma PDP.
Shima shugaban jam'iyyar APC na arewa maso gabas, Salihu Mustapha, ya tofa albarkacin bakin sa inda ya ce canja shekar nashi ya samo asali ne, sakamakon kyawawan ayyukan da jam'iyyar APC keyi.
Sai dai kuma shugaban jam'iyyar PDP na jihar Adamawa, Tahir Shehu, yayi raddi inda ya ce fitar su daga jam'iyyar ba karamin taimako bane a ga jam'iyyar ta PDP.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng