Rikicin Zamfara: Ministan tsaro yayi gargadi akan daukan fansa
- Mansur Dan-Ali ya gargadi mutanen masarautar Zurmi dake jihar Zamfara akan daukan fansa
- Shuagaba Buhari ya umarci ministan tsaro ya tabbatar da an kama mutanen da su kai hari jihar Zamfara
Ministan tsaro, Mansur Muhammad Dan Ali, ya gargadi mutanen masarautar Zurmi dake jihar Zamfara akan daukan fansan ran mutane 35 da aka kashe musu kwananan.
Ministan tsasro, wanda shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya umarce ya kai ziyara jihar Zamfara dan tabbatar da an kama mutanen da suka yi wannan mumunar aika-aika, ya mika ta’aziyar sa ga mutanen masarautar Zurmi akan mutanen da aka kashe musu.
Mai magana da yawun bakin ma’aikatan tsaro na Najeriya, Kanal Tukur Gusau, yayi kira da mazauna garin, da kada su gaza wajen cigaba da ba shugaban kasa, Muhammadu Buhari, goyon baya da hadin kai saboda yana da ikon kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
KU KARANTA : Karya ne ba a wawure dala miliyan $350 na wutan Lantarki – Inji Fashola da Adeosun
A makon da ya gabata ne wasu da ake zargi 'yan bindiga ne, suka kashe mutane 35 a harin da suka kai wa kauyen Birane cikin karamar hukumar Zurmi.
Idan aka tuna baya Legit.ng ta rawaito labarin yadda 'yan bindiga suka kashe mutane 24 da cinnawa gidajen jama'a da dama wuta a jihar Zamfara a watan Nuwamba ta bara.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng