PDP tayi babban rashi bayan Aminin Jonathan ya sauya sheka zuwa APC
- Jam’iyyar PDP tayi babban rashi na magoya baya a Jihar Adamawa
- Ahmad Gulak da wasu jiga-jigai 16 sun tsere daga Jam’iyyar adawa
- Akalla mutane 42, 000 su ka fice daga PDP zuwa APC a karshen mako
Wani na-kusa da tsohon Shugaban kasa Dr. Goodluck Jonathan a da watau Ahmad Gulak ya tattara kayan sa bayan ya fice daga Jam’iyyar adawa ta PDP ya koma Jam’iyyar APC mai mulki a Adamawa.

Asali: Twitter
Sama da mutane 17 wanda ake ji da su a PDP su ka fice zuwa APC a jiya Asabar. Kwanan nan ne dama ake sa rai Shugaban kasa Buhari zai kawo ziyara Jihar ta Adamawa. Har mai ba Jonathan shawara a kan harkokin siyasa Ahmad Gulak ya sauya sheka zuwa APC.
KU KARANTA: Obanikoro yayi lale maraba da yaron sa zuwa APC
Bayan nan kuma akwai manya a Jam’iyyar ta PDP irin su Cif Felix Tangwami, da Cif Medan Teneke, da Alhaji Sahabo Aliyu da Alhaji Saidu Aliyu da su ka tsere daga Jam’iyyar. Sama da mutane 42, 000 ne su ka bi ‘yan siyasar zuwa Jam’iyyar ta APC a Jihar a kwanan nan.
Gulak ya bayyana cewa kokarin da wannan Gwamnati ta APC tayi wa Jihar Adamawa da ma Yankin Arewa maso gabas ta sa su ka bar PDP. Shugaban APC a Yankin Mustafa Salihu ne ya karbi sababbin shiga Jam’iyyar inda ya fada masu tsarin su kuma yayi murna.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng