Kashe-kashen Jihar Zamfara na neman ya fi karfin Jami’an tsaro
- Kwanan nan aka kashe dinbim Jama’a a Garin Birane
- Sufetan ‘Yan Sanda yace abubuwan na nema su gagara
- Sarkin da Gwamnan Garin sun nemi ‘Yan Sanda su dage
A makon jiya ne mu ka samu labari cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe dinbin mutane a Garin Birane a Jihar Zamfara. Yanzu haka barnar na neman ta fi karfin Jami’an tsaron ‘Yan Sandan kasar.
Wannan ta’adi na nema ya gagari Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya inji Sufetan Kasar watau Ibrahim Idris wanda yace za su zurfafa bincike a kan abin da ya faru. Idris ya bayyana wannan ne a gaban Sarkin Zurmi bayan aukuwar abin.
KU KARANTA: Bukola Saraki ya kai ziyara wajen Buratai na rashin Mahaifin sa
Sufetan ‘Yan Sanda ya tashi har zuwa fadar Sarki Mai martaba Abubakar Muhammad. Sarkin ya bayyana cewa sama da ‘yan bindiga 200 su ka shiga harbe mutane a gidajen su a ranar da abin ya faru ya kuma nemi agajin Gwamnati.
Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar Daily Trust, a jawabin da Sufetan ‘Yan Sandan yayi ya nuna cewa abubuwan na nema su wuce tunanin su. Gwamna Yari wanda aka wakilta ya nemi ‘Yan Sanda su kari kokari wajen tsare jama’a.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng