Kashe-Kashe: Hukumomin tsaro sun gaza a jihar Zamfara - Yari
Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara, ya tuhumi hukumomin tsaro na kasa baki daya wajen gazawar su na kare kisan gilla a jihar sa, bayan ankarar da su awanni 24 gabanin afkuwar harin a karamar hukumar Zurmi da ya salwantar da rayuka 39.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin da ya jagoranci tawagar wasu gwamnonin biyar na Arewa zuwa fadar mai martaba sarki Zurmi domin jajinta masa.
Gwamna Yari yake cewa, hukumomin tsaro na yankin su suka gaza wajen kare matsalolin 'yan sara suka da kuma 'yan ta'adda da suka addabi yankin.
A nasa jawabin, Sarkin Zurmi Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa, jarumtar masu tsaron sa kai ne suka fuskanci wannan 'yan ta'adda wanda da yanzu wani labarin ne ba wannan ba.
KARANTA KUMA: Kashe-Kashe: Shugaba Buhari ya aika da ministan tsaro jihar Zamfara
Abubakara yake cewa, 'yan ta'adda 600 sun yi ƙoƙari mamaye garin na Zurmi, sai dai sadaukai na masu tsaron sa kai ta taka muhimmiyar rawar gani.
A yayin haka kuma, jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, a ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya aika da ministan tsaro jihar ta Zamfara domin yin nazari akan harin da ya afku.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng