Bankin Duniya ta amince da ba wa Najeriya bashin $486m don bunkasa wutan lantarki
- Bankin ta bayar da wannan sanarwa ne a ranar juma'a
- Ta ce bashin zai taimaka wurin bunkasa wutan lantarki a Kasar
- Masana kuwa sun nuna cewar wadatuwar wutan lantarki zai habaka tattalin arzikin Kasar
A ranar juma'a ne Bankin Duniya ta sanar da cewar ta amince da ba wa Najeriya jimillan bashi na darajar $486 miliyan domin bunkasa wutan lantarkin Kasar.
Bankin ta bayyana cewar bashin zai taimaka wurin habaka samar da wutan lantarki da kuma rarrabashi don amfanin al'umma.

KU KARANTA: Hukumar 'Yansanda ta kama kungiyar ma su garkuwa da mutane da satar shanu
Rashin samuwa da walwalan wutan lantarki ya gamu da fashin baki daga masana tattalin arziki a inda su ke cewa rashin yalwar sa ya yi wa tattalin arzikin Kasar takunkumi.
Kasancewar wutan lantarki bai yalwata a Kasar ba ya tilasta jama'a da dama amfani da janareta don samun wutan lantarki. Hakazalika yawancin kasuwanci sun dogara ne a kan wutan janareta.
Kudi ne ma su yawan gaske a ke kashewa wurin amfani da janareta idan a ka kimanta shi da farashin wutan lantarki, wanda hakan cikas ne ga habakan tattalin arziki.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng