Mun gana da shugaba Buhari ne domin yaba masa bisa nada Tinubu da yayi a matsayin mai sulhu – Gwamnonin APC
- Gwamnonin APC sun bayyana kudirinsu na zuwa Daura
- Shugaban gwamnonin APC, Gwamna Rochas Okorocha na Imo, ya karyata rahotannin cewa sun kai ziyarar ne domin sanya shugaban kasar sake neman takara
- Okorocha ya kara da cewa gwamnonin APC sunyi amfani da damar wajen yaba ma Buhari bisa nada Asiwaju Bola Tinubu a matsayin mai sulhunta rigingimu a tsakanin yan jam’iyya
Gwamnonin APC a ranar Juma’a sunce kudirinsu na zuwa Daura jihar Katsina shine domin suyi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ta’aziyan rashin yan uwansa guda biyu da yayi.
Shugaban gwamnonin APC, Gwamna Rochas Okorocha na Imo, ya bayyana hakan lokacin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan wata ganawar sirri tare da shugaban kasa Buhari a gidansa na Daura a ranar Juma’a.
Ya karyata rahotannin cewa sun kai ziyarar ne domin sanya shugaban kasar sake neman takara.
Ya ce gwamnonin APC sunyi amfani da damar wajen yaba ma Buhari bisa nada Asiwaju Bola Tinubu a matsayin mai sulhunta rigingimu a tsakanin yan jam’iyya.
KU KARANTA KUMA: Ba a ga Ortom, Ambode, da Amosun ba yayinda gwamnonin APC suka isa Daura domin ziyartan Buhari
Idan bazaku manta ba a makon da ya gabata ne shugaban kasar ya nada Tinubu a matsayin mai sasanta yan jam’iyya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng