Gwamnatin Buhari na amfani da farfaganda a mulkinta – Inji Jonathan
- Tsohon shugaban kasa yace Gwamnatin Buhari na amfani da farfaganda a mulkinta
- Ya zargi gwamnatin APC da gaza cika alkawaran da ta dauka
Rahotanni sun kawo cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya zargi gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari da yin amfani da farfaganda wajen tafiyar da mulkinta kamar yadda ta yi d farfaganda wajen lashe zabe a 2015.
Jonathan ya yi nuni da cewa gwamnatin APC ta kasa cika alkawurran da ta daukarwa 'yan Najeriya a lokacin yakin neman zabe.
Sannan kuma ya kalubalanci jam'iyyar PDP kan ta jajirce wajen kawo karshen mulkin APC a zabe mai zuwa.
KU KARANTA KUMA: Gobe Asabar 17 ga watan Fabrairu zaiyi daidai da zagayowar ranar haihuwar Uwargidan shugaban kasa Aisha
Abaya Legit.ng ta rahoto cewa Gwamnonin jam’iyyar APC sun isa Daura domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Gwamnonin sune: Rochas Okorocha na Imo, Atiku Bagudu na Kebbi, Abdulaziz Yari na Zamfara, Abdulfatai Ahmed na Kwara, Abdullahi Ganduje na Kano, Aminu Tambuwal na Sokoto da kuma Yayaha Bello na jihar Kogi.
Sauran sun hada da: Tanko Almakura na Nasarwa, Abiola Ajimobi na Oyo, Sani Bello na Niger, Godwin Obaseki na Edo. Gwamna Samuel Ortom na Benue, Akinwunmi Ambode na Lagos da kuma Ibikunle Amosun na Ogun basu samu zuwa ba inda mataimakansu suka wakilce su.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng