Gobe Asabar 17 ga watan Fabrairu zaiyi daidai da zagayowar ranar haihuwar Uwargidan shugaban kasa Aisha
Gobe Asabar 17 ga watan Fabrairu zaiyi daidai da zagayowar ranar haihuwar Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha.
An haifi Aisha Buhari wacce ta fito daga jihar Adamawa a ranar 17 ga watan Fabrairu a shekarar 1971, inda a yanzu take da shekaru 47 a duniya.
Aisha ta kasance mata ga shugaban kasa Buhari tun bayan rabuwarsa da matarsa ta farko marigayiya Safina.
Haka zalika Aisha ta kasance mace mai kishin kasa da al’umman kasar, musamman yadda ta jajirce wajen ganin ta tallafawa mutane musamman mata domin ganin sun zamo masu dogaro da kai.

Tana yara hudu da shugaban kasar wadanda suka hada da Halima, Yusuf, Zahra da kuma auta Hanan.
KU KARANTA KUMA: Duk da kisan da akayi wa mutanen jihar Zamfara, gwamna Yari ya yi zaman sa a Abuja
Muna taya uwargidan shugaban kasa murnar zagayowar ranar haihuwarta!
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng