Duk da kisan da akayi wa mutanen jihar Zamfara, gwamna Yari ya yi zaman sa a Abuja
Rahotanni sun kawo cewa kwanaki uku bayan da aka yi wa al’ummar jihar Zamfara kisan-gillar mutane 41, gwamnan jihar Abdul’aziz Yari yayi zamansa a Abuja bai ko leka gida ba.
Kamar yadda kuka sani Yari shi ne Shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya, kuma har zuwa yau Juma’a 16 ga watan Fabrairu bai ziyarci jihar tasa ba.
Wasu maharan da ake zargi barayin shanu ne, su ka kai wa kauyen Birane hari, kuma suka kashe mutanen. Birane na cikin karamar hukumar Zurmi.
Kakakin Rundunar ‘Yan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu, ya ce tun da farko, wasu ‘yan farauta ne daga kauyen Birane su ka bi sawun wani barawon shanu a daji.
Ya ce sun same shi da shanu da tumaki, amma sai suka yi sakacin da ya arce. Bayan ya gudu ne sai ya tsallaka cikin Karamar Hukumar Isa, da ke jihar Sokoto, ya dawo tare da zugar makasa kan babura masu yawa.
Jaridar Vanguard ta ruwaito wani ganau ya ce makasan a kan Babura su ka yi wa kauyen dirar-mikiya, inda ba su yi wata-wata ba, sai suka bude wuta har suka kashe mutane 41.
Silar rikicin ya faro ne bayan rikicin ya kaure ne tsakanin wasu ‘yan farauta da wasu mutane a dajin Birane da suka zarga barayin shanu ne.
Masu farautan sun kama wani mutumi ne da suke zarge sa da satan shanu, inda bayan sun nemi yayi musu bayani kan inda ya samu wannan shanu da yawa sai arce da gudu.
KU KARANTA KUMA: Ba a ga Ortom, Ambode, da Amosun ba yayinda gwamnonin APC suka isa Daura domin ziyartan Buhari
Shehu ya ce ko da suka iso dajin gawar mazaunan kauyen Birani ne kawai suka tadda sai dai ma’aikatan su za su tabbatar sun kamo duk wanda yake da hannu a wannan harin.
Wani dan jarida da ke zaune a jihar Zamfara ya ce makasan sun sake komawa kauyen a ranar Alhamis, inda suka kara kashe mutane da dama.
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma'a ya aika da ministan tsaro, Birgediya Janar Mansur Dan-Ali mai ritaya, zuwa jihar Zamfara domin nazartar halin da ake cikin a kauyen Birane na karamar hukumar Zurmi da aka yi kisan mutane a ranar Alhamis din da ta gabata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng