Kisan mutane 41 a Zamfara: Bamu tabbatar da kashe kashen ba, a Rediyo muka ji – Gwmanatin jihar Zamfara
Kimanin kwanaki uku kenan da wasu yan bindiga suka hallaka mutane da yawansu yah aura mutm 40 a jihar Zamfara, amma haryannzu gwamnan jihar, Abduk Aziz Yari bay a jihar, inji rahoton Premium Times.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamna Yari ya yi tafiya zuwa babban birnin tarayya Abuja tun a ranar Talata, inda ya halarci taruka da daban daban matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.
KU KARANTA: Bera da ɓarna: Beraye sun tafka ma manoman shinkafa mummunar ta’asa a jihar Kebbi
Yan bindiga sun kai harin ne a ranar Laraba a kauyen Birane dake cikin karamar hukumar Zurmi, Inda suka kashe mutane 18, kamar yadda Kwamishinan Yansandan jihar ta bakin Kaakakinsa Muhammad Shehu ya tabbatar.
“Matsalar ta samo asali ne lokacin da wasu mafarauta suka tare wasu barayin shanu da ke neman wucewa ta kauyen Birani, ashe ko da barayin shanun suka tsere, zuwa suka yi suka hado gungun barayi yan uwansu daga karamar hukumar Isah.
“A ranar 14 ga watan Feburairu ne suka dira kauyen, inda suka kaddamar da harin mai kan uwa da wabi, kuma aka samu mace mace daga kowanne bangare.” Inji shi.
Sai dai da majiyar mu ta tuntubi kwamishinan watsa labaru na jihar, Sanda Danjari kan batun, sai yace “Ni ma a rediyo na saurara, na yi kokarin jin ta bakin gwamnan amma ban same shi ba, har sai na tabbatar da labarin daga bakin gwamnan.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng