Ana haihuwar jarirai 140m a duk shekara - WHO
Cibiyar lafiya ta duniya wato World Health Organisation WHO, ta bayyana cewa ana haihuwar jarirai 140m a duk shekara, kuma mafi akasarin haihuwar tana zuwa ne ba tare da wata tangarda wajen uwa ko kuma abinda ta haife ba.
Nothemba Simelela, shugaba ta reshen iyalai, mata da kuma kananan yara a cibiyar, ita ta bayyana hakan a yayin da take bayar da sabbin tsare-tsare da matakan kula wajen nakuda da kuma da zarar an haihu.
Ma'aikaciyar ta WHO take cewa, manufar wannan sabbin matakai ita ce takaita amfani da hanyoyi masu hatsari wajen gaggauta nakuda da saukaka radadi na haihuwa.
Nothemba ta ci gaba da cewa, bai wa mace dama na zabin wanda zai tsaya akan ta yayin nakuda yana daya daga cikin matakai da cibiyar ta tsara bayan bincike na kwararrun lafiya da cibiyar ta gudanar.
KARANTA KUMA: Dalilin da yasa muka gaza cika alkawuranmu - Osinbajo
Binciken cibiyar ya kuma bayyana cewa, akwai kimanin mata 830 dake mutuwa a yayin haihuwa a kowace rana a fadin duniya.
Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, kotu ta gurfanar da wasu makiyaya biyu da laifin kisan gilla a jihar Neja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng