Dubi hotunan kayayakin da jami'an Kwastam suka kwace a jihar Ogun
Hukumar yaki da masau fasakwabri na kasa Kwastam ta yi nasarar dakile wasu masu shigo da kayayaki ta barauniyar hanya a jihar Ogun.
A sanarwan da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Maiwada A.A ya bayar ta shafin facebook, ya ce jami'an rundunar da ke aiki a yankin rafin Ibeji-Idogo-Ifoyintendo sun yi nasarar kama wata motan alfarma kirar Toyota Highlander (2014) daga hannun masu fasakwabri inda har jami'in hukumar ya raunana.
Ya kuma ce a makonni biyu da suka wuce, Jami'an hukumar sunyi nasarar kwace motoci na hannu 13, babura 21, buhunan shinkafa 1,168, jarkunan man gyada takalma da kuma jakunan hannu.
KU KARANTA: NAPTIP ta ceto mata 14 daga hannun masu fataucin mutane
Haza zalika, ya ce jami'an hukumar ba za suyi kasa a gwiwa ba wajen gudanar da ayyukan su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng