Gwamnoni masu barin gado da ke sa-in-sa da Jam’iyyar su saboda kujera a 2019

Gwamnoni masu barin gado da ke sa-in-sa da Jam’iyyar su saboda kujera a 2019

- Akwai Gwamnonin da ke rikici domin kakaba Magaji bayan sun bar kujera

- Daga ciki akwai Gwamnan Ekiti Fayose wanda ke shirin barin mulki a bana

- Gwamnonin sun dage sai sun kakaba wanda zai maye gurbin su idan sun tafi

Mun kawo wasu Gwamnonin Kasar nan da ke rikici da wasu ‘Yan siyasa a cikin Jam’iyyar su saboda rikicin kujerar su. Wasu na harin kujerar yayin da masu shirin barin gadon ke kokarin kakaba Magajin su da kan su.

Gwamnoni masu barin gado da ke sa-in-sa da Jam’iyyar su saboda kujera a 2019
Gwamna Okorocha na neman nada surukin sa a 2019

1. Ayo Fayose

Ko da yake Gwamnan na Ekiti zai bar mulki ne a bana, yana kokarin nada Mataimakin sa Farfesa Olusola Kola a matsayin Gwamna. Da dama daga cikin har na kusa da Gwamnan sun kalubalace sa.

KU KARANTA: Masu neman takarar Gwamnan Ekiti sun kai karar Ayodele Fayose

2. Abiola Ajimobi

Gwamnan Jihar Oyo, Ajimobi na shirin barin gado a 2019 kuma ana tunani akwai wanda yake neman dorawa. Hakan ya sa ake sa-in-sa da Ministan sadarwa Adebayor Shitu wanda ke neman kujerar.

3. Rochas Okorocha

Yanzu haka ana fama da Gwamann Imo Okorocha wanda yake kokarin tsaida Surukin sa takara. Gwamnan na neman ganin Mijin ‘Diyar sa wanda yana cikin manyan wannan Gwamnati sun gaje sa. Jama’a da dama dai sun nuna cewa ba za su hakan ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng