Saraki ya kai wa iyalan Buratai da tsohon Sakataren Gwamnati gaisuwa
- Bukola Saraki da sauran Sanatoci sun kai wa Janar Tukuar Buratai ta'aziyya
- Shugaban Majalisar Dattawan ya kuma yi wa iyalin wani tsohon SGF gaisuwa
- Kwanakin bayan Shugaban Hafsun Sojojin kasar Buratai ya rasa Mahaifin sa
A jiya Alhamis ne mu ka samu labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Dr. Bukola Saraki ya kai wa Shugaban Hafsun Sojin kasar nan watau Laftana-Janar Tukur Buratai ta'aziyya na Mahaifin sa da ya rasu a cikin 'yan kwanakin baya.
Bukola Saraki ya kai ziyara wajen Tukur Buratai na rashin Mahaifin sa Malam Yusuf Buratai da yayi a makonnin da su ka wuce inda aka yi Marigayin adduar Allah yayi masa rahama. Saraki ya bayyana wannan a shafin sa na Tuwita.
KU KARANTA: Sojoji sun sa tukwuici kan Abubakar Shekau
Shugaban Majalisar kasar Bukola Saraki da sauran takwarorin sa Sanatoci irin su Shehu Sani sun kuma kai wa iyalin tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya Marigayi Mallam Gidado Idris wanda ya rasu a can baya gaisuwa duk a ranar.
Idan ba ku manta ba kwanakin baya Sufeta Janar na 'Yan Sanda Ibrahim Idris da wasu manyan kasar sun kai wa Janar Tukur Yusuf Buratai gaisuwa a wajen zaman makoki. Mahaifin Sojan ya rasu ne yana da shekaru sama da 100 a Duniya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng