Wani dan jarida ya ci na jaki a hannun 'dan sanda a harabar majalisar dokiki
- Wani dan jarida ya ci na jaki a hannun 'dan sanda a harabar majalisar dokiki
- Kungiyar 'yan jaridar jihar sun fitar da kakkausar sanarwa inda suka yi Allah-wadai da lamarin
Labarin da muke samu daga majiyar mu ta tabbatar mana da cewa jami'in dan sandan Najeriya dake shiyyar jihar Akwa ibom a jiya Laraba ya lakadawa wani dan jarida mai suna Mista Samuel Ayara dukan tsiya a harabar majalisar dokokin jihar.
KU KARANTA: Yan hizba sun kama mabarata 8 a jihar Kano
Kamar dai yadda labarin ya zo mana, dan sandan da ya bugi dan jaridar sunan sa Sunday Agada kuma yana aikin gadin dan majalisar jihar ne mai wakiltar karamar hukumar Ikot Abasi mai suna Mista Uduak Udoudo.
Legit.ng ta samu cewa tuni shugabannin kungiyar 'yan jaridar jihar suka fitar da kakkausar sanarwa inda suka yi Allah-wadai da lamarin sannan kuma suka bukaci majalisar ta yi bincike sannan ta kuma hukunta dukkan wanda aka samu da laifi.
Haka zalika ma Wani tsohon jami'in rundunar 'yan sandan Najeriya da ya kai matsayin mataimakin Sifeto Janar kafin ritayar sa mai suna Alhaji Raimi Odofi ya bayyana goyon bayan sa ga batun da yanzu haka ake cigaba da tafka muhawara kan sa na kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya.
Alhaji Odofi dai ya yi wannan ikirarin ne a yayin da yake zantawa da wakilin majiyar mu a gidan sa dake a garin Ibadan, jihar Oyo dake a kudu maso yammacin Najeriya.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng