'Yan fashi sun caccakawa wata tsohuwa mai shekaru 75 wuka, sun harbi danta a Kano
- Wasu 'yan fashi a garin Babawa, karamar hukumar Gezawa, a Kano sun caccakawa wata tsohuwa wuka tare da harbin dan ta
- 'Yan fashin sun dira gidan da tsohuwar, Hajiya Abu Haruna, da dan ta Alhaji Yakubu Haruna, ke zaune da misalin karfe 3:00 na daren jiya
- Yanzu haka tsohuwar da dan ta na asibitin Murtala inda suke samun kulawar jami'an aikin lafiya
A daren jiya ne da misalin karfe 3:00 wasu da ake zargin 'yan fashi ne suka haura gidan wani mutum, Alhaji Yakubu Haruna, inda yake zaune tare da mahaifiyar sa a garin Babawa dake karkashin karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.
'Yan fashin sun caccakawa tsohuwar, Hajiya Abu Haruna, mai shekaru 75 wuka kafin daga bisani su harbi dan nata, Alhaji Yakubu, a kafa.
Dan uwa ga Alhaji Yakubu ya shaidawa wakilin jaridar Daily Trust cewar yanzu haka dan uwansa da aka harba na samun kulawa a asibitin kwararru na Nasarawa dake Kano yayin da Hajiya Abu ke samun kulawa a asibitin Murtala dake birnin Kano bayan anyi mata tiyata.
DUBA WANNAN: 2019: Zan samar wa Buhari kuri’u miliyan biyar a Kano – Gwamna Ganduje
Da yake tabbatar da faruwar al'amarin, kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Kano, Magaji Musa Majiya, ya ce babu wanda ya rasa ransa cikin mutanen da 'yan fashin suka raunata.
Kazalika ya bayyana cewar hukumar bata kama kowa ba dangane da afkuwar lamarin tare da sanar da cewar tuni kwamishinan 'yan sandan jihar, Rabi'u Yusuf, ya bayar da umarnin yin bincike a kan lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng