Buhari zai isa Kaduna yayinda rundunar sojin sama ke kaddamar da jirgin yaki wanda aka kera a Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai isa jihar Kaduna a yau, Alhamis, 15 ga watan Fabrairu domin kaddamar da wani jirgi wanda rundunar sojin saman Najeriya ta kera.
Jirgin Tsaigumi UAV shine na farko da rundunar sojin saman Najeriya ta fara kerawa a gida.
Legit.ng ta tattaro cewa za a kai shi yankin arewa maso gabas bayan an kaddamar dashi domin yaki da ta’addanci.
Sashin bincike da ci gaba na hukumar NAF inda aka kera jirgin sun taka gagarumin rawa karkashin jagorancin shugaban hafsan sojin sama, Air Vice Marshal Saddique Abubakar.
A halin da ake ciki Jam’iyyar PDP tace shawarar da babban jigon jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu ya bayar na cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Babangida(mai ritaya) su janye daga siyasa sannan su bi sahun kungiyar masu ritaya yafi dacewa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.
KU KARANTA KUMA: Ya kamata Buhari ma ya bi sahun masu ritaya – PDP ga Tinubu
Jam’iyyar tace shawarar Tinubu ya gasgata matsayar Obasanjo, Babangida, jam’iyyar PDP dama yan Najeriya da dama “wadanda suka tsaya kan cewa kada Buhari ya sake neman takara a 2019, saboda ya gaza a gwamnatinsa da kuma kasa hada kan kasa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng