N-Power: Gwamnatin Tarayya ta gargadi matasa dasu kula da 'yan damfara a yanar gizo

N-Power: Gwamnatin Tarayya ta gargadi matasa dasu kula da 'yan damfara a yanar gizo

- An Gargadi matasa da su lura da labaran bogi a yanar gizo

- Ana ta yada labarai a yanar gizo na cewar N-Power zata sake daukan maikata

- An bukaci matasa da su guji bawa wasu kudi da nufin sama musu aikin yi

N-Power: Gwamnatin Tarayya ta gargadi matasa dasu kula da 'yan damfara na yanar gizo
N-Power: Gwamnatin Tarayya ta gargadi matasa dasu kula da 'yan damfara na yanar gizo

Gwamnatin Tarayya ta gargadi matasa da su kula sosai da 'yan damfara a yanar gizo, wadanda suke ikirarin zasu bawa matasa aikin N-Power.

DUBA WANNAN: Yadda aka kashe General Murtala Muhammad

Wata sanarwa da Babban mai taimakawa Mataimakin Shugaban Kasa, akan harkar samar da ayyuka, Mista Afolabi Imoukhuede, ya tabbatar da cewar babu wata sanarwa da ta fita wacce ta ke nuna cewar Gwamnatin Tarayya ta sake bude shafin ta N-Power.

Ya kara da cewar duk wani bayani da aka fitar wanda yake da alaka da bude shafin N-Power na yanar gizo karya ne, 'yan damfara ne suke son yaudarar mutane.

Ya bukaci 'yan Najeriya dasu dinga lura da labaran karya a yanar gizo, sannan su dinga bin shafin N-Power na gaskiya domin samun labari ingantacce.

Sannan gwamnati ta gargadi masu son cika aikin N-Power din, da kada su sake su bawa wani lambar Bank Verification wato (BVN) a takaice, sannan kuma kada su bawa wani ko wata kungiya kudi da nufin zata nema musu aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng