Rasuwan yan Makaranta: Wannan ba karamin jarabawa bane a kanmu - Gwamna Jihar Bauchi
Wannan kalami ya fito a bakin Mai girma Gwamna Jihar Bauchi Mohammed A. Abubakar Esq, yayin kawowa da gabatar da ta'aziyar sa a fadar Mai Martaba Sarkin Misau ga iyaye, iyalai, "yan uwa, abokan arziki, Karamar Hukumar Misau, Masarautar Misau dama Jiha baki daya.
A cigaba da jawabin sa, Mai girma Gwamna ya nuna matukar Alhinin sa, bisa wannan rashi da jarabawa da ya sauka a wannan sati cikin wannan Jiha.
Yayi addu'ar Allah ya sada mu da wadannan yara a Jannatul Firdausi, su kuwa wadanda basu da lafiya Allah ya basu lafiya.
Wannan sati dai ya kasance satin da zai shiga cikin tarihin Masarautar Misau da Jihar Bauchi baki daya. Hakan ya faru ne sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da yaran wata makaranta 20 da Malaman su 2 da direban motan.
KU KARANTA: Ku daina yada tsoro da janyo tashin hankali a kafofin watsa labaru – Gwamnatin tarayya
Mai Martaba Sarkin Misau Alh. Ahmad Sulaiman Mni, yayi godiya ne a madadin iyaye, iyalai, "yan uwa da abokan arziki ga Mai girma Gwamna bisa wannan karamci wanda yasa ya bar aiyukan dake gaban sa yayi tattaki yazo don mika ta'aziyar sa da jajanta mana wannan al'amari da muka samu kanmu ciki na rashin "yan asalin Masarautar.
Sannan a karshe an gabatar wa Mai girma Gwamna Shugaban Makarantar, iyayen wadanda suka rasu, sunayen wadanda suka rasu da wadanda suke jinya kamar yadda zan rubuto su a kasa.
*SUNAYEN MALAMAI
*Mal. Moh'd Moh'd Ya rasu
*Malama A'ishatu Moh'd Jarwal Ta rasu
*Mal. Moh'd Inuwa Yana jinya
DALIBAI
Kasim Ibrahim Yana jinya
Isma'il Adamurasu Ya rasu
Hajara Garba Ta rasu
Babangida Chidawa Ya rasu
Abubakar A. Adamu Ya rasu
Aliyu Mohammed Ya rasu
Al-Amin A. Liman Ya rasu
Hauwa Mohammed Ta rasu
Ni'ima Aliyu Salihu Ta rasu
Fatima Mohammed Ta rasu
Fatima Ibrahim Ta rasu
Amina Auwal Ta rasu
Fatima Isma'il Ta rasu
Usman Abba Ya rasu
Fatima Adamu Ta rasu
Mustapha Abdullahi Ya rasu
Hadiza Nalado Aliyu Ta rasu
Kawu Idris Ya rasu
A'isha Moh'd (Low Cost)Ta rasu
Ibrahim Babayo Ya rasu
Sai Direban mota Ya rasu
Allah Yaji qansu da Rahama.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a
Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa Da Kuma
Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng