NYSC: Gwamnatin Jihar Enugu ta karawa Malaman asibiti albashi

NYSC: Gwamnatin Jihar Enugu ta karawa Malaman asibiti albashi

- Masu yi wa kasa hidima za su samu karin albashi a Enugu

- Gwamnatin Jihar za ta sakawa masu bautar kasa a Kauyuka

- Kwamishinan Jihar yace hakan zai sa matasa su zage dantse

Gwamnatin Jihar Enugu ta bayyana cewa za ta kara alawus din da ta ke ba masu bautar kasa a a asibitoci da dakunan shan magani a cikin kauyuka a fadin Jihar domin karfafawa aikin na su.

NYSC: Gwamnatin Jihar Enugu ta karawa Malaman asibiti albashi
Gwamnati za ta karawa masu NYSC alawus a Enugu

Kwamishinan yada labarai na Jihar Enugu Mista Ogbuagu Anikwe ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa za su kara albashin Likitoci zuwa N30, 000. Haka kuma sauran Malaman asibiti za su rika tashi da N20, 000 a kowane wata.

KU KARANTA: Gwamnati za ta samawa dinbin matasa aikin yi Najeriya

Anikwe ya tabbatar da wannan ne bayan taron Majalisar zartarwa na Jihar da aka yi a makon nan. Kawo yanzu dai ba wani abu Malaman asibitin da ke yi wa kasa hidima watau NYSC ke tashi da shi ba a Kauyukan Jihar.

Gwamnatin Jihar Enugu tace wannan zai sa duk shekara a rika kashe sama da Naira Miliyan 30 wanda Jihar na gani cewa akwai bukatar inganta harkar kiwon lafiya a Jihar. Masu bautar kasa dai na yawan gudun zama a kauye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng