Boko Haram: Rundunar Sojin Najeriya ta tare mota cike da bama-bamai

Boko Haram: Rundunar Sojin Najeriya ta tare mota cike da bama-bamai

- Sojojin Najeriya na cigaba da tarwatsa ‘Yan Boko Haram har a Dajin Sambisa

- Rundunar Sojin kasar sun kwakwulo ‘Yan ta’adda a Ajingi, Talala da Malunti

- Bayan nan kuma an ci karfin ‘Yan ta’addan a wani Gari a can cikin Jihar Borno

Rundunar Sojojin OPERATION LAFIYA DOLE ta yi nasarar tare da motar ‘Yan ta’addan da ke cike da bama-bamai. An kuma samu wasu kayan ‘yan ta’ddan da su ka hada da tuta da abin hawa.

Boko Haram: Rundunar Sojin Najeriya ta tare mota cike da bama-bamai
Sojojin Najeriya sun koyawa 'Yan Boko Haram hankali

Sojojin Kasar sun dace inda masu sintirin Operation DEEP PUNCH II su ka ci karo da mota cike da kayan kunar bakin-wake a jiya Laraba a Garin Buni Yadi da ke cikin Jihar Yobe. Nan ne aka yi ba ta-kashi tsakanin ‘Yan ta’dda da Sojojin kasar.

KU KARANTA: Manyan Sojojin Najeriya sun kai wa Janar Buratai ziyara

Manjo Nureni Alimi na Bataliyar Sojojin kasar yace sun tare mota cike da kayan kunar bakin-wake bayan sun samu labarin cewa ‘Yan ta’addan na kokarin tserewa. Bayan zuwan Sojojin ne ‘Yan ta’addan su kayi kokarin tserewa bayan sun ji wuya.

‘Yan ta’addan na Boko Haram sun ci kafar kare su ka bar motocin su a nan. Sojojin Kasar sun yi nasarar tarwatsa bama-baman da ke garkame cikin motar. Kwanan nan ma dai an casa wasu ‘Yan ta’ddan da su ka burma hannun Sojoji a Garin Goniri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng