INEC ta ja kunnen ma'aikata game da karban cin hanci
- Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta ja kunnen bata garin ma'aikata
- Hukumar ta ce duk wanda aka samu yana karbar cin hanci kafin yiwa mutane rajisat sai gamu da fushin hukuma
- INEC ta bukaci al'umma su kawo karar duk wanda suka samu yana aikata wannan laifin
Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na jihar Legas, Mista Sam Olumekan ya yi gargadi ka ma'aikatar hukumar kan karbar na goro kafin gudunar da aiyukan da aka dauke su don yi.
Ya ce hukumar ta INEC ba za ta sasauta wa masu saba doka ba babban zaben 2019 mai zuwa.
A yayin da ya ke jawabi ga manema labarai jiya a Legas, Olamekun ya ce an gano cewa wasu ma'aikatan hukumar na karbar kudi daga al'umma kafin su musu rajistan zabe.
KU KARANTA: Hukumar Sojin Najeriya ta shawarci Shekau ya mika wuya
Shugaban ya ce hukumar ta fara sa ido domin gano masu aikata irin wannan aikin kuma za su dandana kudar su.
"Matsalar da mutane ke fama da ita shine wasu ma'aikata na karbar cin hanci kafin suyi wa al'umma rajista.
"Tabbas duk ma'aikacin da aka kama yana karbar cin hanci kafin ya yi wa mutane rajista zai hadu da fushin hukuma. Dai dace mutum ya biya komai ba kafin ayi masa rajista. Ina kira da al'umma su kawo karar duk masu irin wannan dabi'ar." inji shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng