Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnatin tarayya ta aika da ma'aikatan NSCDC 1600 don kare garkunan shanu

Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnatin tarayya ta aika da ma'aikatan NSCDC 1600 don kare garkunan shanu

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da wani sabon shiri akan ma'aikatan hukumar NSCDC a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, domin tunkara tare da kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Babban jami'i mai jagorantar wannan shiri, mataimakin kwamanda na reshen, Adamu Soja ya bayyana cewa, za a aika da ma'aikatan hukumar guda 1600 domin bayar da kariya ga garkunan shanu daga barayi.

Shugaban yake cewa, su na da bukatar kayan aiki kama daga motoci zuwa makamai da zasu taimaka wajen sauke nauyin da rataya a wuyansu.

Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnatin tarayya ta aika da ma'aikatan NSCDC 1600 don kare garkunan shanu
Rikicin makiyaya da manoma: Gwamnatin tarayya ta aika da ma'aikatan NSCDC 1600 don kare garkunan shanu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, ma'aikatan za su rinka gewaye a kan dawakai a wuraren da motoci ba su da ikon kutsawa wajen kare gonaki da kuma garkunan shanu.

KARANTA KUMA: Cututtuka 8 da ka iya shafe duniya cikin kiftawar idanu

Legit.ng ta fahimci cewa, bayan kaddamar da wannan shiri a jihar Zamfara, ma'aikatan za kuma su kutsa jihohin Kaduna, Neja, Taraba, Kogi da kuma Nasarawa domin kawar da shakku tare da fargaba ta al'umma wajen samun tsaro a gonakin su da kuma garkunan su na shanu.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne, babbar kafar watsa labarai ta talabijin wato NTA, ta karrama shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu, dangane da jajircewar sa da kuma zakakuranci sauke nauyen da rataya a wuyansa na ci gaban kasa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng