Kabilar Fulani suna cikin kunci fiye da sauran kabilu a Najeriya - Maigamo
- Alhaji Abdullahi Maigamo ya ce babu kabilar da tafi Fulani fuskantar kuncin rayuwa a Najeriya
- Maigamo ya bukaci shugabbanin Najeriya da su saukar da hakkokin Fualin da ya rataya a wuyan su
Babban Akaunta Janar na jihar Bauchi, Alhaji Abdullahi Maigamo, yace kabilan Fulani sun fi kowace kabila fuskaNta kuncin rayuwa a Najeriya.
Yace sauran kabilu sun fi Fulani cin ribar romon dimokradiyya wanda haka bai kamata ba, ya kamata a rika adalci a tsakanin duka kabilu a kasar.
Alhaji Abdullahi Maigamo ya bayyana hakan ne a lokacin da ke jawabi a wajen wani taron da ya shirya wa ‘yan uwan sa Fulani domin tattaunawa kan muhimman matsalolin dake ci wa Fulani tuwo a karya da nufin shawo kansu da aka gudanar a IBB Square da ke jihar Bauchi.
Alhaji Abdullahi, Maigamo yace, yana son ya zaburar da shugabanni akan hokkokin Fulani da ya rataya wuyan su.
KU KARANTA : Ku daina yada tsoro da janyo tashin hankali a kafofin watsa labaru – Gwamnatin tarayya
“A cikin dukkanin kabilun da suke cikin Najeriya babu kabilar da take cikin kunci raywu kamar kabilar Fulani.
“Don haka muka kawo wa gwamnan jihar mu kukanmu domin ya yi mana ayyuka kamar yadda ake yi wa sauran mutane”.
Daga cikin bukatun da Fulani suka gabtar wa gwamnan ya hada da hada da samar wa shanun ruwan da abinci.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku ci gaba da bin mu a
Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa
Da Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng