An tsaurara matakan tsaro yayin gurfanar Shema gaban kotu
- An gurfanar da tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shema, gaban wata kotun Najeriya dake Katsina
- Shema da wasu mutane uku na fuskantar tuhumar cin amana da almundahanar kudi, biliyan N11bn
- An tsananta tsaro a harabar kotun yayin bayyanar tsohon gwamna Shema a jiya, Talata
An tsananta tsaro a babbar kotun Katsina a jiya yayin da aka ci gaba da sauraron karar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta shigar da tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema.
Hukumar EFCC ta gurfanar da Shema tare da Hamisu Makana, Lawal Ahmad Safana, da Ibrahim Lawal Dankaba bisa zarginsu da cin amana da kuma sama da fadi da kudin jama'a da yawansu ya kai biliyan N11bn.
Kotun ta dakatar da sauraron karar a watan Fabrairu na shekarar 2017 bayan lauyan Shema ya kalubanci hurumin kotun na sauraron karar a gaban wata kotun daukaka kara dake Kaduna, wacce ita kuma ta mika maganar gaban kotun koli ta tarayya.
Saidai kotun kolin ta ki amincewa da bukatar lauyan Shema tare da umartar kotun da ta ci gaba da sauraron karar.
DUBA WANNAN: Akwai makiya dimokradiyya cikin ministocin Buhari - Saraki
Bayan sauraron jawaban lauyoyin kowanne bangare, alkalin kotun, Ibrahim Maikaita, ya tsayar da ranakun 10, 11, da 12 ga watan Afrilu domin cigaba da sauraron karar.
Gwamnatin jihar Katsina ce karkashin gwamna Aminu Masari, dan jam'iyyar APC, ta gayyaci hukumar EFCC domin ta kwato kudaden jihar da tayi zargin tsohon gwamna Shema dan jam'iyyar PDP da wawure wa daga asusun jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng