Da dumi-dumi: Jirgin Delta Air ya kama da wuta a cikin hazo

Da dumi-dumi: Jirgin Delta Air ya kama da wuta a cikin hazo

A safiyar yau, Asabar 14 ga watan Fabrairu, jirgin Delta Air yayi saukan gaggawa a babba filin jirgin saman Murtala Mohammad dake Legas jim kadan bayan ya kama da wuta a cikin hazo.

Matukin jirgin Delta Air flight DL055 (ATL)ETG da ya lura da haka ya tuntubi ma’aikatan jirgin saman Legas domin bukatan saukan gaggawa. Da wuri aka kira jami’an kashe wuta domin kawar da wannan annoba.

Bayan sun samu daman sauka cikin lafiya, dukkan fasinjojin jirgin sun fita da wuri domin tsiratar da rayukansu.

Da dumi-dumi: Jirgin Delta Air ya kama da wuta a cikin hazo
Da dumi-dumi: Jirgin Delta Air ya kama da wuta a cikin hazo

Duk da cewan babu rayukan da aka rasa a yanzu, wasu fasinjoji da ma’aikatan jirgin saman sun ji rauni kuma an kaisu asibitin koyarwan jami’ar jihar Legas Ikeja, asibitin hukumar sojin sama, da asibitin FAAN.

KU KARANTA: Neymar zai yi gaba da gaba da Ronaldo

A bangare guda, an kulle filin jirgin saman na kimanin sa’a daya yanzu. Wannan kuma ya shafi sauran jiragen da sukayi shirin tashi.

Jiragen KLM, Lufthansa da Air France sun shirya tsaf domin shiga hazo amma an hanasu tashi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel