Kotu ta wanke likitan tsohon shugaba Jonathan daga zargin rashawar kudi

Kotu ta wanke likitan tsohon shugaba Jonathan daga zargin rashawar kudi

- Wata babban kotu da ke Abuja tayi watsi da karar tuhumar rashawa da aka shigar kan likitan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

- A yayin da ya ke zartar da hukunci, Mai shariah Peter Affen ya ce masu tuhumar basu samar da gamsasun hujoji da ke nuna cewa wanda ake tuhuma ya aikata rashawar ba

- Affen ya ce masu tuhumar sun kasa kawo wa kotu shaidar cewa wanda ake tuhuma ma'akacin gwamnati ne

A ranar Talata 13 ga watan Faburairu ne wata babban Kotu da ke Abuja tayi watsi da karar da aka shigar kan likitan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Fortune Feberesima na tuhumar sa da aikata rashawa.

Kotu ta wanke likitan tsohon shugaba Jonathan daga zargin rashawar kudi
Kotu ta wanke likitan tsohon shugaba Jonathan daga zargin rashawar kudi

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, Hukumar EFCC ta zargi Fiberesima da laifin bayar da kwangilar kudi naira 258.8 miliyan da kuma naira 36.9 milyan a wata kamfani da yake da hannun jari wadda hakan ya sabawa dokar kasa na 12 da 19 na dokar rashawa da ayyukan da sukayi kama da rashawar na 2000.

KU KARANTA: Wasu 'yan PDP sun kafa sabuwar kungiya, sun lissafo da hanyoyi 6 don gyara Najeriya

Sai dai Alkalin Kotun, Mai shariah Peter Affen ya ce hukumar ta EFCC ta gaza samar da hujja na nuna cewa wanda ake tuhuma ma'aikacin gwamnati ne saboda haka ya yi watsi da karar.

Affen ya kara da cewa tsohon shugaban kasar ya nada shi ne kawai a matsayin likitan sa a siyasan ce amma ba'a dauke shi aiki a matsayin ma'aikacin gwamnati ba.

A wata rahoton kuma, Legit.ng ta ruwaito cewa hukumar ICPC ta kama wani Alkalin kotun Afil mai murabus, Mai Shari'ah Mohammed Tsamiyya bisa zargin sa da neman cin hanci a kan shariar dan majalisar dattawa a jihar Imo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164