Alhamdulillah: Allah ya ceto rayuwar wani jigon jam’iyyar PDP daga hannun masu garkuwa da mutane

Alhamdulillah: Allah ya ceto rayuwar wani jigon jam’iyyar PDP daga hannun masu garkuwa da mutane

Wani jigon jam’iyyar PDP a jihar Kaduna, kuma tsohon ma’ajin kudi na jam’iyyar Alhaji Musa Danbaba Saya-yaya ya tsira da ransa daga hannun miyagu masu garkuwa da mutane, inji rahoton Daily Trust.

Idan za’a tuna Legit.ng ta ruwaito yaronsa, Aliyu Musa yana fadin yan bindigan sun dira gidansu ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar Talata, 13 ga watan Feburairu, cikin wasu manyan motoci guda biyu, inda suka yi awon gaba da mahaifinsa.

KU KARANTA: Jam’iyyar PDP ta shiga halin dimuwa, masu garkuwa da mutane sun cika hannu da wani Jigonta

Wannan lamari ya faru ne bayan yan bindigan sun yi harbe harbe a kauyen Saya-yaya dake cikin karamar hukumar Ikara na jihar Kaduna, inda Musa ke zaune da iyalinsa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

shima Kaakakin rundunar Yansandan jihar Kaduna, Mukhtari Aiyu ya tabbatar da lafiyar Danbaba, inda yace da misalign karfe 7 na yammacin talata, 13 ga watan Feburairu ne Allah ya kubutar da mutumin.

ASP Mukhtari yace a yanzu haka Danbaba na cikin koshin lafiya, kuma yan bindigan basu taba lafiyar jikinsa ba.

“Bani da cikakken bayani dangane da lamarin kubutarsa, don a yanzu haka jami’an mu suna tattaunawa da shi, amma da zarar sun kammala da shi, zan baku karin haske game da yadda ya tsira.” Inji shi ga manema labaru.

Daga karshe ya yaba ma jama’a da suka taimaka musu da bayanan sirri, tare da mika godiyar rundunar bisa hadin kan da suke samu daga garesu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng