Wata Bokanya ta shiga hannu bayan ta yi sanadiyyar mutuwar Uwargidar wani ɗan majalisa
Jaridar Daily Trust ta ruwaito jami’an rundunar Yansandan jihar Katsina sun yi caraf da wata mata mai sana’ar bokanci, Sakina, kan zarginta da yin sanadin mutuwar uwargidar wani dan majalisa.
Ita dai wannan uwargida, mai suna Binta Safiyanu, ma tace ga dan wani wakili a majalisar dokokin jihar Katsina, dake wakiltar al’ummar mazabar Musawa, Yunusa Idris Jikamshi.
KU KARANTA: Barka: Likitoci sun samu nasarar raba wasu jarirai da aka haifa manne da juna a Bauchi
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hajiya Binta, mahaifiyar yara har guda shida, ta nemi bokanyar ce ta bata maganin gargajiya, wanda za ta sha, kuma ya bulbulo mata da ruwan mama, don ta shayar da jariranta yan biyu.
Sai dai, jim kadan bayan ta sha maganin, sai kawai ta fara haraswa, cikin mintuna 10 ta ce ga garinku nan, inda aka garzaya da ita asibitin garin Musawa, a can likitoci suka tabbatar da mutuwar matar, kuma tuni aka yi mata jana’iza.
Da fari, maganar na hannun ofishn Yansandan garin Musawa ne, amma a yanzu an mika maganan ga sashin bincken manyan laifuka na rundunar Yansandan jihar don cigaba da bincike.
A yanzu haka Sakina na hannun Yansanda, kuma Kaakakin rundunar, DSP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin, kuma ya bada tabbacin zasu gudanar da binciken kwakwaf game da shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng