Zamu fara haƙar mai daga rijiyoyin mai guda 5 a jihar Bauchi – Inji shugaban hukumar NNPC
Shugaban hukumar kamfanin man fetir na Najeriya NNPC, Maikanti Baru ya bayyana cewa tuni sun kammala shirye shiryen fara hako man fetir a jihar Bauchi kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Baru ya bayyana haka ne a ranar Talata 13 ga watan Feburairu, a yayin wata ziyarar da gwamnan jihar Bauchi, MA Abubakar ya kai masa a ofishinsa dake shelkwatar hukumar, a babban birnin tarayya Abuja.
KU KARANTA: Majalisa ta tursasa ma wani na hannun daman Buhari gurfana a gabanta, ya amsa kira
Kaakakin gwamnan jihar Bauchi, Shamsuddeen Lukman ya bayyana dalilin ziyarar da gwamna Abubakar ya kai, shi ne domin jinjina ma shugaban hukumar NNPC bisa jajircewar da ya nuna wajen tabbatar da binciko arzikin man fetir a jihar Bauchi.
Da yake jawabi a yayin ziyarar, Maikanti ya bayyana ma gwamna Abubakar da tawagarsa cewa a yanzu hukumar NNPC ta kammala shirye shiryen fara hako mai a rijiyoyin danyen mai guda biyar ta hanyar amfani da na’uroin zamani, dukkaninsu a yankunan Alkaleri na jihar Bauchi.
Shi ma gwamna MA Abubakar yace zai bada hadin kai dari bisa dari don ganin an samu nasara kokarin hakar man da hukumar NNPC, wanda ya bayyana matakin a matsayin wata kafa da zata jefa jihar Bauci cikin jihohi masu arzikin man fetir.
Idan za’a tuna, a shekarar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarni ga hukumar man fetir ta kasa, NNPC, da ta duba yiwuwar hako mai a yankin Arewacin kasar nan.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng