Siyasar Kano: Babu yadda za’ayi na yarda Kwankwaso ya dinga juya ni – Gwamna Ganduje

Siyasar Kano: Babu yadda za’ayi na yarda Kwankwaso ya dinga juya ni – Gwamna Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya bayyana cewar tarihin siyasar sa ba zata cika ba ba tare da ambatan sunan tsohon Maigidansa ba, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Kwankwaso.

The Cable ta ruwaito Ganduje ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da yayi da yan jaridu a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, yayin wani taron tsaro daya gudana.

KU KARANTA: Wani kwamandan Boko Haram ya gamu da daurin shekaru 60 a gidan Yari

Majiyar Legit.ng ta ruwaito gwamnan wanda ya gaji Kwankwaso a matsayin gwamnan jihar Kano a shekarar 2015, yana cewa shi da Kwankwaso aminai ne a baya, amma alakarsu ta yi tsami a yanzu.

Siyasar Kano: Babu yadda za’ayi na yarda Kwankwaso ya dinga juya ni – Gwamna Ganduje
Kwankwaso da Gwamna Ganduje

“Ya kamata ku sani, a baya aminai ne mu, na kud da kud, in takaice muku zance, tarihina ba zai cika ba har sai an ambaci sunan Sanata Kwankwaso, haka zalika tarihin siyasar Kwankwaso ba zata cika ba sai an ambaci sunana.

“Amma mun samu matsala, saboda mun san cewa dolen dole a siyasa wata rana sai mutum ya kai matsayin da babu wanda zai juya shi, ku kanku kun san hakan zai yi wuya, duba da halayyar shuwagabanni” Inji Ganduje.

Da yake karin haske game da zargin kananan yara sun kada kuri’a zaben kananan hukumomi da ya gudana a jihar Kano a ranar Asabar, Ganduje ya musanta zarge zargen, inda yace batanci ne da farfaganda.

“Duk farfaganda ce, kuna iya tuntubar masu sa idanu da suka ziyarci jihar daga sassan kasar nan, don haka ba ma sai mun yi ta mayar da martani game da wadannan zarge zarge ba, mun san akwai masu hada hotuna da bidiyo a kafafen sadarwa na zamani.” Inji shi.

Daga karshe Ganduje ya bayyana zaben a matsayin mai inganci, sa’annan ya nuna farin cikinsa bisa nasarar da jam’iyyarsa ta APC ta samu.

Dangantaka ya fara tsami ne tun bayan da mahaifiyra gwamnan jihar Kano ta rasu, kuma tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng