Yayin neman yalwar ruwan mama, matar wani dan majalisa ta sha tsimi ta sheka lahira

Yayin neman yalwar ruwan mama, matar wani dan majalisa ta sha tsimi ta sheka lahira

Tsautsayi da hausawa kan ce ba ya wuce ranar sa ya afkawa matar wani dan majlisar dokoki na jihar Katsina, Binta Safiyanu, wadda ta riga mu gidan gaskiya a yayin da ta sha wani tsimi domin samun yalwar ruwan mama don wadatar da jariranta.

Wannan mata dai ta rasu ta bar 'ya'ya shidda, bayan mako guda da haife tagwayen ta.

Kafar watsa labarai ta Northern City ta ruwaito cewa, marigayi Binta itace uwargidan dan majalisa Yunusa Jikamshi, mai wakilcin mazabar Musawa a majalisar dokoki ta jihar Katsina.

Rahotanni sun bayyana cewa, bayan haihuwar tagwayen ne ta bukaci yalwar ruwan mama da zai wadatar da jariranta, inda bisa ga shawarar abokan zamanta biyu ta diddiki wani tsimi domin biya mata wannan bukata.

Marigayiya Binta Safiyanu
Marigayiya Binta Safiyanu

A halin yanzu dai, hukumar 'yan sanda ta tsananta bincike kan wannan lamari, inda tuni tayi ram da daya daga cikin kishiyoyin ta, domin kuwa su suka tabbatar da mata da ingancin wannan tsimi na gargajiya.

KARANTA KUMA: Hotunan ganawar shugaba Buhari da tsohon shugaba Abdulsalami

A wani sabanin rahoto kuma, marigayi Binta ta saba shaye-shayen tsimi da magungunan garjiya.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, shan wannan tsimi ke da wuya marigaya ta fara kwarara amai, inda aka yi gaggawar mika ta babban asibiti na garin Musawa kuma daga bisani ta ce ga garin ku nan.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, dan majalisar Dattawa Dino Melaye, ya lashi takobbi kan ci gaba da fadin gaskiya da sukar kowace gwamnati muddin ta aikata rashin daidai ba tare da fargaba jefa shi gidan kurkuku ba kamar yadda gwamnatocin baya suka saba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: