Yadda Matar Jonathan ta hada Dala Miliyan 11.4 ba tare da wata sana’a ba
- Mutane sama da 30 su ka jefa Dala Miliyan 11.4 cikin asusun Dame Jonathan
- Hukumar EFCC na nema a daskare wadannan akawun din na Matar Jonathan
- Ita kuwa Patince Jonathan ta nemi a sasanta da Hukumar EFCC a wajen Kotu
Mun samu rahoto daga Jaridar The Nation inda aka jero mutanen da su ka jefa makudan kudi na Miliyoyin Daloli cikin asusun Mai dakin tsohon Shugaban kasa watau Dame Patience Jonathan. A yanzu dai Jonathan na kokarin sasantawa ne da EFCC.
Daga cikin wadanda su ka zuba Daloli a asusun tsohuwar Uwargidar kasar akwai Festus Iyoha, Ocheche Emmanuel, Philemon Buoro, Festus Isidahomen, Felicia Apatke, Patricia Okogun, Buoro Ojo, Stella Wasiu, Amaka Adebayo da Segun Moses.
KU KARANTA: Kotu ta gagara zama domin cigaba da shari’a tsakanin EFCC da Patience
Bayan su kuma akwai Jimoh Peter, Ahmad Musa, Ibrahim Musa, Dame P. Jonathan, Ayemere Sunday, Eneji AP, Johnson Ojo, Mary Buoro, Jude Bosede, Festus Iyoha, Jimoh Moses, Ahmed Musa, Germaine, Dudafa, Germani, Ade Sulaiman, Kunle Peter.
Ragowar su ne Muhammad Adamu, Francis Muhd, da Ado Suleiman. Yanzu dai wadannan kudi da aka saka a akawun din ta sun haura Dala Miliyan 11.4 don haka EFCC ke nema a rufe asusun Uwargidar tsohon Shugaban kasar. Yanzu haka dai an dage karar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng