Nigerian news All categories All tags
Najeriya da kasar Koriya ta Arewa zasu kulla sabuwar alaka don tabbatar da tsaro da zaman lafiya

Najeriya da kasar Koriya ta Arewa zasu kulla sabuwar alaka don tabbatar da tsaro da zaman lafiya

Shugaban kasar Koriya ta Arewa, ya yi alkawarin hada karfi da karfe da Najeriya don samar da dawwamammen zaman lafiya da tsaro, kamar yadda jakadan kasar a Najeriya, Jong Yong Chol ya bayyana.

Jakadan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar a yayin bikin cikar tsohon Shugaban kasar Kim Jong-II, cika shekaru 76, da ace yana raye, a babban birnin tarayya Abuja, inji rahoton Guardian.

KU KARANTA: Ina tsoron fushin ubangiji – Inji wani babban Fasto da ke neman yan mata da Mata mabiyansa

Jakada Chol ya bayyana Kim a matsayin shugaba da ya sadaukar da ransa ga al’ummarsa tare da tabbatar da zama lafiya a Duniya gaba daya, a cewarsa marigayin ne ya dabbaka alaka tsakanin kasar Koriya da Najeriya, wanda a yanzu kasashen na cin gajiyar alakar.

“Muna fatan cigaba da kyautata alaka da hadin kai tsakanin Najerita da Koriya, muna fatan cigaba da tabbatar da zamanlafiya da tsaro, musamman a yanzu da dansa, kuma shugabanmu, Kim Jong Un ya gaje shi wajen yada zaman lafiya.” Inji shi.

Daga karshe ya yi fatan samun nasarar Najeriya a yakin da ta ke yi da ta’addanci, da kuma matsalar cin hanci da rashawa.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito an haifi marigayi Kim a ranar 16 ga watan Feurairu shekarar 1942, kuma ya mutu yana da shekaru 69 a shekarar 2011.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel