An gano Shekau shigar mata yake yi ya tsere da an kewaye shi

An gano Shekau shigar mata yake yi ya tsere da an kewaye shi

- Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa azaba ya yi shugaban Boko Haram tsanani kuma yana neman hanyar guduwa

- A sanarwa da hukumar Sojin ta bayar, Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau yana batar da sahu ne ta hanyar sanya hijabi

- Hukumar sojin ta yi kira ga mazauna jihohin Borno, Adamawa da Yobe su sanya ido kan mazaje masu shiga irin ta mata

Hukumar Sojin Najeriya ta samu ingantacen bayannan sirri da ke nuna cewa shugaban yan ta'adda kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fara batar da sahun sa ne ta hanyar sanya hijabi kamar yadda mata keyi.

An gano Shekau shigar mata yake yi ya tsere da an kewaye shi
An gano Shekau shigar mata yake yi ya tsere da an kewaye shi

Kakakin rundunar ta soji, Birgediya Janar Sani Usman wanda ya bayar da wannan sanarwan a ranar Talata, ya kuma ce wuya ce tayi ma Shekau yawa har ya tsere ya bar mabiyan nasa.

KU KARANTA: Badakalar bacewar kudi a JAMB: Shehu Sani ya bayar da mafita

"Azaba ne tayi masa yawa, a halin yanzu yana kokarin neman hanyar da tsere ne kuma ya yi shiga irin na mata sanye da hijabi.

"Wata majiya ingantaciya ta sanar da mu cewa yana amfani da hijabi baki ko kuma shudi. An ganin da akayi masa na karshe yana sanye da bakar hijabi ne.

"Muna kira ga sauran yan kungiyar Boko Haram su ajiye makaman su, su fito daga inda suka boye, idan sukayi hakan zamu karbe sunu biyu-biyu," inji Usman.

Usman ya kara da cewa rundunar sojin na cigaba da tsananta bincike domin kamo shugaban na kungiyar ta Boko Haram, ya kuma yi kira ga al'ummar jihohin Borno, Yobe da Adamawa su sa ido kan mazajen da ke shiga irin na mata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164