An shawarci masu ciki dasu yawaita saduwa da mazajensu domin saukin haihuwa
- Mata masu ciki na bukatar motsa jiki da saduwa, inji wani likita
- Saduwar tana kara baiwa hanyar jaririn fadi da yalwa
- Saduwar takan hanzarta kawo nakuda da ma saukin haihuwa musamman dab da haihuwa
Wani kwararren likitan Gynae a Abuja, Dakta Chris Agboghoroma ya bayyana cewa yawan saduwa da namiji ga mace mai ciki musamman lokacin da ta kusa haihuwa na taimakawa wajen hanzarta kawo nakuda da saukin haihuwa.
Likitan, ya bayyana kiwon cikin da soyayya a matsayin muhimman abubuwa da mace zata yi la'akari dasu yayin ciki da ma saukarta.
A wurin wasu dai, sukan dauka ba daidai bane a sadu da mace, musamman idan cikinsu yayi nauyi, da ma dauka lallaba jikinsu shi zai kawo haihuwa cikin sauki.
Hawan jini, kiba, da ma kiba kan karu ga masu ciki, musamman a lokutan da suka kai tarago na biyu da na uku lokacin rainon ciki.
DUBA WANNAN: Anyi kira ga INEC da ta soke zabukan kananan hukumomi a Kano
A cewarsa; a lissafe kamata yayi mace mai ciki ta haihu cikin makonni 38 ko 42 amma saboda wasu matsaloli ta kan wuce wannan lokaci.
Ya kara da cewa mace mai ciki za ta iya guje wa irin haka idan tana saduwa da mijin ta akai-akai idan ta kusa haihuwa.
Bayan haka ya karyata wannan camfe-camfen da ake yadawa wai babu kyau mace ta sadu da mijin ta idan tana da ciki, musamman Idan ta kusa haihuwa.
Bari ku ji ma, rashin haka matsala yakan jawo wa mace Idan ta zo haihuwa.
Kafin ya kammala bayanan sa, likitan ya yi kira ga ma’aurata da su maida hankali wajen sanin matsayin mahaifar matan su yana mai cewa macen da ke da budadiyyar mahaifa yawan saduwa da ita Kan sa tayi barin cikin, amma Idan ba haka ba saduwa lokacin mace na da ciki lafiya ce.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng