Kasuwar bukata: Bayan rubuta wasika ga Buhari, ana kallon-kallo tsakanin magoya bayan Babangida da na Obasanjo

Kasuwar bukata: Bayan rubuta wasika ga Buhari, ana kallon-kallo tsakanin magoya bayan Babangida da na Obasanjo

- Tsofin shugabannin kasa; Obasanjo da Babangida sun rubuta budaddiyyar wasika ga shugaba Buhari a kwanakin baya

- Obasanjo ya kafa wata kungiya (CMN) da yake fatan zata rikide ta koma jam'iyyar siyasa

- Magoya bayan Babangida sun nuna shakkun su a kan kungiyar tare da kokarin hana ubangidan su marawa kungiyar baya

Bayan sun rubuta budaddiyyar wasika ga shugaba Buhari a lokuta daban-daban, tsofin shugabannin kasa; Obasanjo da Babangida ba zasu hadu karkashin inuwa daya ba, kamar yadda wani na kusa da Babangida ya shaidawa jaridar The Nation.

Wasu makusanta da iyalin Babangida sun nuna rashin amincewar su ga hada karfi da sabuwar kungiyar Obasanjo ta CMN.

Kasuwar bukata: Bayan rubuta wasika ga Buhari, ana kallon-kallo tsakanin magoya bayan Babangida da na Obasanjo
Babangida da Obasanjo

Manyan yaran Babangida irinsu tsohon mai bawa shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Janar Aliyu Gusau (mai ritaya), tsohon sakataren jam'iyyar PDP, Ben Obi, da tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa, Birgediya Halilu Akilu mai ritaya, sun gana da Babangida a garin Minna a kan hakan.

Ya zuwa yanzu Babangida da magoya bayansa da suka har da dan cikinsa, Mohammed Babangida, na neman mafita dangane da makomar su a siyasance.

DUBA WANNAN: Waiwaye adon tafiya: Mata ne ke mulkin masarautar Daura kafin zuwan Bayajidda, Duba jerin sunayen su

Wasu daga cikin dalilan da magoya bayan ke bayar wa na kin hada karfi da Obasanjo shine irin yadda shi Obasanjo ya wulakanta Mohammed Babangida ta hanyar bincikar sa lokacin yana shugabancin kasa.

Wani bincike ya tabbatar da cewar Babangida magoya bayansa na kulle-kullen kafa Mohammed ya zama gwamnan jihar Neja. Saidai hakan ya zo da sarkakiya domin gwamnan jihar mai ci dan tsohon soja ne sannan suruki ne ga tsohon shugaban kasa Abdulsalam Abubakar.

Hakan ya saka yanzu sun yanke shawarar tsayar da Mohammed takarar Sanata a zabe mai zuwa da niyyar zai nemi takarar gwamna a shekarar 2023.

Wata majiya ta bayyana cewar tun a shekarar 2015 magoya bayan Babangida suka so Mohammed ya tsaya takarar gwamna amma hakan bata yiwu ba.

Abin jira a gani shine matsayar da magoya bayan Babangida zasu cinma kafin a kada gangar siyasar 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng