Gaba kura baya hayaki: Matan da aka kubutar daga hannun kungiyar Boko Haram na cikin halin tsaka wuya
- Kungiyar Boko Haram ta dade tana sace mata tare da amfani da su wajen tayar da bama-bamai
- A kwanan nan hukumar sojin Najeriya ta kubutar da wasu mata masu yawa daga hannun kungiyar ta Boko Haram
- Matan da aka kubutar sun bayyana cewar har yanzu jama'a na yi masu kallon 'yan kungiyar Boko Haram
Kamar yadda rahotanni Legit.ng ke kawo maku, mayakan kungiyar Boko Haram sun dade suna sace 'yan mata tare da amfani da su wajen tayar da bama-bamai.
A kwanakin nan dakarun sojin Najeriya sun kubutar da mata da dama da kungiyar Boko Haram ke rike da su.
Wata ma'aikaciyar gidan jaridar BBC, Stephanie Hegarty, ta yi tattaki ya zuwa garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, domin ganawa da irin wadannan mata da aka kubutar daga hannun kungiyar Boko Haram.
Wakiliyar ta BBC ta gano cewar matan da suka kubuta na cikin tsaka mai wuya domin har yanzu al'umma basu karbe su da zuciya guda ba, ana ci gaba da zaman dar-dar da su saboda tsoron cewar sun dade tare da mayakan kungiyar Boko Haram.
DUBA WANNAN: Yadda wani jirgin yakin sojin Najeriya ya yi luguden wuta a maboyar 'yan Boko Haram tare da lalata wata motar su ta yaki (Bidiyo)
Wata matashiya, Fatima, mai shekaru 19 da mayakan kungiyar suka taba sacewa yayin da suka kai hari garin kakanninta da ta kai ziyara, kuma yanzu ta samu kubuta, ta shaidawa Hegarty irin halin da take ciki.
Fatima ta ce, bayan mayakan kungiyar sun tafi da ita sai suka aurar da ita ga wani daga cikinsu. Saidai mijin nata ya mutu a wani gumurzu da sojin Najeriya. Bayan rasuwar mijin nata ne sai mayakan kungiyar suka daura mata bama-bamai suka turo ta garin Maiduguri, inda iyayenta ke zaune, domin kai wani hari.
Fatima ta ce, ita so kawai take ta rabu da mayakan, a saboda haka bata nuna masu ba cewar ba zata aikata abinda suke so ba.
Duk da bata tayar da bama-bamai da aka daura mata ba, Fatima ta ce har yanzu iyayenta da 'yan uwanta na zaman dar-dar da ita saboda dadewar da tayi tare da mayakan kungiyar Boko Haram.
DUBA WANNAN: Hotunan mutane da makaman da Sojoji suka kwato daga hannun kungiyar Boko Haram
Matashiyar ta bayyana jin dadinta bisa kasancewar ta daya daga cikin tsirarun matan da suka samu damar kubuta daga hannun kungiyar Boko Haram tare da bayyana cewar zata ci gaba da rayuwar ta duk da gani-ganin da jama'a ke yi mata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng