Wani Saurayi yayi wa Matan Garin Matazu a Jihar Katsina abin alheri

Wani Saurayi yayi wa Matan Garin Matazu a Jihar Katsina abin alheri

- Wani Masoyin Shugaba Buhari ya ba dinbin Mata jari a Jihar Katsina

- Wannan Matashi yace ba Gwamnati ce kadai za ta taimaki talaka ba

- Hamzah Ukashatu ya kira jama’a masu hali su yi koyi da irin wannan

Mun samu labari na musamman inda wani Bawan Allah masoyin Shugaba Buhari da kuma Gwamna Aminu Masari a cikin Jihar Katsina ya ba dinbin Mata kudi domin tada sana’ar su. Bayan nan kuma za a duba lafiyar jama’a 500 kyauta a Garin.

Wani Saurayi yayi wa Matan Garin Matazu a Jihar Katsina abin alheri
Wani Matashi ya ba Mata jarin kasuwanci a Katsina

Hamza Ukashatu Musa Matazu wanda yake tare da Jam’iyyar APC ya bayyana cewa akwai hakki kan masu hali da su rika taimakawa Jama’a. Malam Hamzah Ukashatu yace ba za a bar Gwamnatin kadai ta cigaba da taimakawa talakawa ba.

Wannan Matashi ya bayyanawa manema labarai cewa bai yi amfani da siyasa wajen raba wadannan kaya ba. Shugaban wannan gidauniyar yace ba ‘yanuwan sa ya jefa a cikin tafiyar ba, yace ya ya nemi marasa karfi ne ya agaza masu.

KU KARANTA: 'Yan fanshi sun harbe wani Bawan Allah a banki

Daga cikin wadannan Mata da aka rabawa wannan gudumuwa a Garin na Katsina, sun yabawa wannan Gwamnati wanda su kace a yanzu sun ji kuma sun gani. Wata saboda tsabar jin dadin wannan abu ta nemi Gwamna Masari yayi shekaru 16 a mulki.

A baya dama kun ji labari cewa Hamzah Ukashatu Musa wanda ya bude wata gidauniya ya ba dinbin Mata masu karamin karfi kayan koyon sana’a da kuma jari na kasuwanci da sauran gudumuwa a Garin Matazu da ke cikin Jihar ta Katsina.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng